Waiwayen Tarihi: Dan boko na farko a birnin Zazzau, Muhammadu Aminu Sambo (1888-1961)

Waiwayen Tarihi: Dan boko na farko a birnin Zazzau, Muhammadu Aminu Sambo (1888-1961)

- Waiwayen tarihin mu na yau zai waiga labarin dan Boko na farko a arewa

- Malam Muhammadu Aminu Sambo (1888-1961) dan boko ne da ya jagoranci Turawan mulkin mallaka shawagin kidaya

- Ya rayu a zamanin mulkin Sarki Ibrahim Kwasau a birnin Zazzau

Waiwayen Tarihi: Dan boko na farko a birnin Zazzau, Muhammadu Aminu Sambo (1888-1961)
Waiwayen Tarihi: Dan boko na farko a birnin Zazzau, Muhammadu Aminu Sambo (1888-1961)

An haifi Malam Malam Muhammadu Aminu Sambo ne a shekarar 1888 a garinn Zazzau, kuma ya rasu ne a 1961. Yana daga cikin samarin farko da Boko ta taras a Zaria, inda ya zama mai jin turanci, kuma dan boko da har sai da ya jagoranci Turawan mulkin mallaka shawagin kidaya.

A shekarar 1923 ya zama dan boko na farko a birnin Zazzau da ya fidda Sarki Kwasau da ma mutan Zariya daga kunya, inda har Sarki Ibrahim dan Kwasau ya nada shi Jagora ga tawagar Birtaniya da Sarki George ya aiko don yin nazarin dukan kabilan arewacin Najeriya lokacin mulkin mallaka.

DUBA WANNAN: Yadda ake wa Kiristoci wayo a amshe musu kudi a coci

A zamanin nan da jama'ar Arewa ke ganin kamar ilimin Boko bashi da wani alfanu, su irin wadannan dattijai sunyi wa kansu kiyamul-laili, inda suka rungumi zamani, kuma zamanin ya karbe su ya tafi tare da su, ba tare da sun yada al'adarsu ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng