Abin yazo: INEC ta fitar da jadawalin kiranyen Dino Melaye

Abin yazo: INEC ta fitar da jadawalin kiranyen Dino Melaye

Hukumar zabe mai zaman kanta na kasa (INEC) ta fitar da jadawalin cigaba da yiwa Sanata Dino Melaye kiranye. Mr. Melaye dan majalisa ne mai wakiltan yankin Kogi ta yamma a majalisar ta dattawa.

Sanarwan fitar da rannakun da za'a gabatar da kiranyen ya fito ne ta hannun sakataren hukumar ta INEC, Augusta Ogakwu a jiya Juma'a.

Kamar yadda jidawalin kiranyen ya bayyana, za'a fara ne da baza sanarwan tattancewa a ofishin hukumar da ke karamar hukumar Lokoja babban birnin jihar ta Kogi a ranar 27 ga watan Maris.

Hakazalika, za'a rufe karaban takardun masu sa ido kan kiranyen a ranar 4 ga watan Afrilu a hedkwatan hukumar da ke babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Gwamnati za ta karbi tubar 'yan Boko Haram da suka mika wuya - Buhari

A ranar 25 ga watan Afrilu, za'a gudanar da taron masu ruwa da tsaki game da kiranyen a ofishin INEC da ke jihar.

Za'a jefa kuri'a na yi masa kiranye ko akasin haka a ranar 28 na watan Afrilu, sannan za'a sanar da sakamakon kuri'ar da al'ummar uankin nasa suka kada a ranar 29 ga watan Afrilu na 2018

Ga dai takarda dauke da yadda hukumar ta tsara gudanar da kiranyen a kasa.

INEC ta sanar da ranar cigaba da yiwa Dino Melaye kiranye
INEC ta sanar da ranar cigaba da yiwa Dino Melaye kiranye

INEC ta sanar da ranar cigaba da yiwa Dino Melaye kiranye
INEC ta sanar da ranar cigaba da yiwa Dino Melaye kiranye

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164