An kori ASP na 'Yan sanda, an kuma yiwa wani murabus
- Hukumar Yan Sandan Najeriya ta kori wani jami'i mai mukamin ASP daga aiki
- Hukumar kuma ta tilasta wa wani ASP din yin murabus na dole
Hukumar ‘Yan Sanda ta kori ASP na ‘Yan Sanda bisa ga aikata babban laifi. Hukumar kuma ta tursasa wani ASP yin murabus na dole, bayan ta tsallake sha’anin kwamitin horaswa a kan DCP, Godwin Nwobodo, inda ta kara masa matsayi zuwa kwamishinan ‘Yan Sanda.
A wani jawabi na ya fito daga mai magana da yawun 'yan sandan, Ikechukwu Ani, yace, Nwobodo a lokacin yana matsayin mataimakin Kwamishinan ayyuka na ‘Yan Sanda, a jihar Osun.
KU KARANTA: Abin yazo: INEC ta fitar da jadawalin kiranyen Dino Melaye
Ya kara da cewa, hakan na cikin shawarar da hukumar tayi a wurin taronsu na 26, da tasukayi a birnin tarayya, wanda ciyaman dinta, Dr. Mike Okiro ya gudanar.
Sanarwan ta cigaba da cewa hukumar ta fasa batun korar wasu ma’aikata biyar, ta kuma mayar dasu bakin aiki. Ta kuma mayar, ta karawa wani DSP matsayi, da kuma wasu ASP guda biyu, bayan sallama da wankesu da kotu tayi.
Sauran matakan da hukumar ta dauka sun hada da ragewa wasu DSP biyu matsayi, da ASP, sannan anyiwa SP, DSP, da ASP biyu gargadi mai zafi da jan kunne, tare da wasu CSP biyu, da SP guda uku.
“Hukumar ta cire wani ACP, sannan ta bawa wani ACP, takardar shawara”, a wani sanarwa da ta fitar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng