Matsayar da muka cinma da kungiyar Boko Haram kafin sakin 'yan matan Dapchi - Lawal Daura

Matsayar da muka cinma da kungiyar Boko Haram kafin sakin 'yan matan Dapchi - Lawal Daura

- Shugaban Hukumar Binciken sirri na SSS, Lawal Daura ya bayyana cewa hukumar tayi sulhu wajen ceto yan matan Dapchi kamar yadda shugaba Buhari ya bayar da umurni

- Daura ya ce yarjejeniyar kawai da suka yi shine na tsagaita wutan na wani dan lokaci saboda a dawo da yan matan

- Daura ya kara da cewa sun tattauna yadda za'a samu mafita don kawo karshen hare-haren baki daya

A yau Juma'a ne babban Direkta na Hukumar Binciken Sirri na kasa (SSS), Lawal Daura ya bayyana cewa hukumar ta SSS tayi amfani da hikimomi na diplomasiyya a maimakon karfin soji wajen ceto yan matan kamar yadda Shugaba Buhari ya bayar da umurni.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, Daura ya shaida wa manema labarai a fadar shugaban kasa cewa anyi ta tattaunawa masu sarkakiya karkashin jagorancin hukumar ta SSS kafin aka sako yan matan.

Yadda muka yi sulhu aka sako 'yan matan Dapchi guda 105 - Lawal Daura
Yadda muka yi sulhu aka sako 'yan matan Dapchi guda 105 - Lawal Daura

A yayin da yake magana a kan irin yarjejeniyar da sukayi da yan ta'addan kafin a saki matan, Daura ya ce ka'idar kawai da suka amince da ita shine tsagaita wuta na wucin gadi wanda zai bawa yan ta'addan dama su dawo da yan matan inda suka dauke su tun da farko.

KU KARANTA: Buhari ya lashi takobin ladabtar da wadanda sukayi sakaci aka sace 'yan matan Dapchi

Daura ya kara da cewa sulhun anyi shi ba wai don ceto 'yan matan Dapchi ne kadai ba amma ana son a kawo karshen hare-haren da yan ta'addan ke kaiwa wasu sassan yankunan ne.

Hakazalika, an tattauna abin da zai faru da yan ta'addan da ke tsare wajen hukuma da kuma sauran yan Najeriya da yan ta'addan ke tsare da su har ma da yiwuwar yin afuwa ga yan ta'addan da ke son mika wuya.

Daura kuma ya yi tsokaci kan yanayin da aka sami yan matan na Dapchi inda ya bayyana cewa da yawan su na fama da matsalolin fatan jiki a dalilin rashin wanka da ba su samun daman yi cikin wata daya da suke tare da yan ta'addan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164