Wani Malami yayi sanadin yanke hannun wani Almajiri sakamakon azabtar da shi da yayi (Hotuna)

Wani Malami yayi sanadin yanke hannun wani Almajiri sakamakon azabtar da shi da yayi (Hotuna)

Wani mummunan lamari mai cike da ban tausayi da ya dauki hankulan jama’a ya faru a tsakanin wani Malamin tsangaya da wani almajirinsa a jihar Gombe, wanda lamari ya bar baya da kura.

Gidan rediyon FM na Progress 97.3 ne ta ruwaito wannan labara mai ban takaici, inda wani malamin tsangaya ya dinga azabtar da daya daga cikin almajirinsa har sai da yayi sanadiyyar guntule masa hannu.

KU KARANTA: Budurwa ta tayar ma uwarta balli kan zargin maita a Benuwe, har sai da suka kashe ta

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a unguwar Kagarawal dake cikin garin jihar Gombe, inda Malamin mai suna Surajo mai tsangaya ya daure ma almajirinsa mai suna Zubairu, hannu da igiyar shanya na tsawon lokaci har sai da hannayensa biyu suka rube

Wani Malami yayi sanadin yanke hannun wani Almajiri sakamakon azabtar da shi da yayi (Hotuna)
Zubairu

A sakamakon halin rai fakwai mutuwa fakwai da yaron ya shiga ne, sai wasu mutane suka garzaya da shi Asibiti, inda likitoci suka tabbatar da babu abinda za yi ma wannan yaron in banda a guntule hannuwan nasa, shi ne saukin kadai da zai samu.

Jama'a sun bayyana ra'yinsa game da haka, kamar haka Hafsat Nuhu tace "Kai Allah ya isarwa wannan yaro,Amma gaskiya yakamata Gwamnati ta shigo wannan Magana ta Yanda zaa hukunta wannan Azzalumin malami."

Hansau Aliyu Abubakar yace: "Allah ya sakamasa,shikuma,azzalumin malamin allah kai ikonka akansa tunda ya zalunci karamin yaro" yayin da Amina Aminu tace "Hmm wannan ba musulunci ba ne, a hukunta wnan malamin."

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng