Sule Lamido ya bayyana babban dalilin da yasa yake muradin ɗarewa kujerar shugaban kasa

Sule Lamido ya bayyana babban dalilin da yasa yake muradin ɗarewa kujerar shugaban kasa

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, kuma tsohon minista a gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Alhaji Sule Lamido ya bayyana dalilin da yasa yake son zama shugaban kasar Najeriya.

Lamido ya bayyana cewar ba kwadayi yasa yake hankoron zama shugaban kasa ba, inda yace muradin bautawa ma yan Najeriya, tare da son gyaran kasar nan yasa yake matukar kaunar zama shugaban kasa.

KU KARANTA: Babban sufetan Yansanda yayi mi’ara koma baya game da batun janye Yansanda dake gadin Attajirai

Kamfanin dillancin labaru NAN, ta ruwaito Lamido ya bayyana haka ne a ranar Alhamis 22 ga watan Maris, a yayin wani taron tattaunawa da yayi da yayan jam’iyyar PDP na jihar Legas, inda ya soki gwamnatin APC, da cewa bata tabuka ma yan Najeriya komai ba, don haka dole su canza ta.

Sule Lamido ya bayyana babban dalilin da yasa yake muradin ɗarewa kujerar shugaban kasa
Sule Lamido

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Lamidon na fadin jam’iyyar APC ta yaudari yan Najeriya da alkawurran da ta daukan musu a yayin yakin neman zabe, da suka hada da yaki da rashawa, samar tsaro da kuma inganta tattalin arziki.

Sa’annan ya bayyana kansa a matsayin cikakken dan jam’iyyar PDP da ya dace ya zama dan takarar jam’iyyar na takarar shugaban kasa a shekarar 2019, duba da dadewarsa a jam’iyyar da sanin siyasar Najeriya.

Daga karshe yayi kira ga yayan jam’iyyar PDP da su hada kansu don kawar da APC a 2019, “Har sai mu yan PDP mun hada kanmu ne zamu iya kawar da APC a 2019, inda kuma muka yi sake APC ta koma mulki, sai Allah ya tambayemu.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng