Yadda Ministan sadarwa yake bushasha da miliyoyi da gidaje 13 a Legas da Abuja
Mun samu labarin cewa ana zargin Ministan sadarwa Adebayor Shittu da rashin biyan Hadiman sa kudin su da bai wuce N250,000 a wata ba duk da cewa ya karbi albashin da ya haura na Miliyan 50 ban da alawus na kusan Dala Miliyan 1.
Wani Bawan Allah Victor Oluwadamilare wanda yake cikin masu ba Ministan sadarwan Najeriya Adebayo Shittu shawara ya zargi mai gidan na sa da toye masa da wani abokin aikin sa Tajudeen Imam hakkin su duk da cewa yana da hali.
Oluwadamilare yayi wannan bayani ne a wata wasika da ta shiga hannun Jaridar Sahara Reporters inda yace yana bin Ministan bashin kudi har Miliyan 13 na aikin da yayi na kusan watanni 30 daga karshen shekarar 2015 zuwa yau.
KU KARANTA: ICPC ta tasa tsohon Gwamnan Jihar Filato a gaba
Wannan mai ba Ministan shawara yace bayan shigan sa Gwamnati ya saye kamfanin buga labarai, ban da motoci 25 da ya saya a leda da kuma gidaje 12. Bayan nan dai Gwamnati ta ba ofishin sa motoci 8 domin zirga-zirgan aiki.
A wasikar, Victor Oluwadamilare ya bayyana yadda Ministan ya rika biyawa yara da manya rututu kujerar aikin Hajji. Duk da wannan facaka da barna da kudi, an zargi Ministan sadarwar da rashin biyan Hadiman sa kudin aikin su.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu alabaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng