Zan yiwa Ganduje da duk masu taimkonsa a siyasance ritaya daga siyasa - Kwankwaso

Zan yiwa Ganduje da duk masu taimkonsa a siyasance ritaya daga siyasa - Kwankwaso

Sanatan Kano ta tsakiya kuma tsohon gwamnan jihar, Rabi'u Musa Kwankwaso, ya ci alwashin yiwa gwamna Ganduje da duk masu taimkonsa a siyasance ritaya daga siyasa.

A wani faifan sauti da gidan Radiyon Express dake Kano su ka yada jiya, Laraba, Kwankwaso ya bayyana cewar babu wani sulhu da zai saka shi canja alwashin da ya ci a kan gwamnan.

Tsohon gwamnan ya ce cin amanar da Ganduje ya yi masa ya isa ya saka shi kayar da shi a zaben 2019.

Zan yiwa Ganduje da duk masu taimkonsa a siyasance ritaya daga siyasa - Kwankwaso
Ganduje da Kwankwaso

Kazalika, Kwankwaso, ya dauki alkawarin koyawa duk wani mai kokarin taimakon Ganduje a siyasance darasi koda kuwa mutum a Abuja yake.

An rawaito Kwankwaso na cewar "Ku je Ku rubuta ku ajiye cewar na fada maku zan yiwa maci amana da 'yan koronsa ritaya daga siyasa."

DUBA WANNAN: Kalaman Bill Gates a kan gwamnatin Buhari: Elrufa'i ya mayar da martani

An dade ana gugar zana da musayar shagube tsakanin tsohon gwamna Kwankwaso da magajinsa, gwamna Ganduje.

A yayin auren diyar Ganduje da dan gwamna Ajimobi na jihar Oyo, an rawaito Kwankwaso na cewar marasa aikin yi ne zasu bata lokaci halartar daurin auren zawarawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng