Ku roki Allah ya yi min zabi mafi alkhairi - Dalibar Dapchi ta aiko wa mahafiyar ta da wasiyya
- Mahaifiyar yarinyar da Boko Haram suka rike don ta ki karabar musulunci, Mrs. Sheribu ta ce diyar nata ta aiko musu da sako lokacin da za'a taho da sauran yaran
- Mrs. Shuaibu ta bayyana cewa Leah ta bayar da sakon cewa a cigaba da yi mata addu'a ga Ubangiji ya tabbatar da ikon sa game da rayurwar ta
- Iyayen Leah sun mika rokon su ga gwamnatin tarayya da ta taimaka wajen ganin cewa mayakan na Boko Haram sun sako diyar ta su
Mahaifiyar 'yar makarantar Dapchi da Boko Haram suka rike don ta ki karbar musulunci, Mrs. Rebecca Sheribu ta ce diyar ta, ta aiko da sako inda ta ce mahaifiyar ta da sauran yan uwan ta su cigaba da yin addua'a ga Ubangiji ya tabbatar da ikon sa game da rayuwar ta.
Kamar yadda kafar yadda labarai na The Nation ta ruwaito, mahaifiyar Leah ta shaida wa manema labarai a garin Dapchi cewa har yanzu bata cire rai da dawawar diyar ta ba inda ta kara da cewa za ta cigaba da yin adduo'i ga Ubangiji ya dawo mata da diyar ta lafiya.
KU KARANTA: Muhimman Abubuwa 10 da ya kamata ku sani a kan sabon mataimakin gwamnan CBN
Majiyar Legit.ng ta gano cewa mahaifiyar Leah ta yanke jiki ta suma yayin da mayakan Boko Haram suka dawo da yan matan amma bata ga diyar ta ba. Yan kungiyar na Boko Haram sun rike yan matan har na tsawon wata daya.
Duk da cewa Mrs. Sheribu ta farfado sumar da tayi, har yanzu kullum tana cikin rashin walwala ne duk da cewa al'umma suna ta zuwa yi mata jaje da kuma bata hakuri bisa rashin sako diyar ta da ba'ayi ba.
"Yan matan da aka sako sun ce yan ta'addan sun ce dole Leah ta karbi musulunci kafin su sako ta amma ta fada musu cewa bata san komi game da musulunci ba saboda haka ba za ta iya zama musulma ba. Hakan ya suka rike ta wai har sai rannan da ta musulunta.
"An ce mana an bar Leah tare da wasu mata guda uku kuma anan ne ta bayar da sakon cewa a mu cigaba da yin addua'a ga Ubangiji ya zartar da ikon sa game da rayuwarta," inji Mrs. Sheribu.
Daga karshe iyayen Leah, Mr. Nathan Sheribu da mahaifiyar diyar sunyi kira ga gwamnati ta taimaka don ganin an sako diyar na su kuma sunyi godiya da mutanen garin bisa irin gudunmawa da suke basu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng