A raba aure tsakani na da Mijina, bai taba Sallah ba tun bayan aurenmu– Inji Uwargida
Wata dambarwa irin ta ma’aurata ta faru a gaban Kotun shari’ar Musulunci dake Magajin Gari na jihar Kaduna, inda wata mata ta zargi Mijinta da rashin yin Sallah tun da suka yi aure, don haka Kotu ta raba aurensu.
Matar mai suna Yahanasu Dahiru mai shekaru 23 ta bayyana ma Kotun cewar mijinta Nasiru Sani ba shi da hali nagari, mutumin banza ne kuma baya sallah kwata kwata, bata taba ganinsa yana yi ba tun bayan da suka yi aure.
KU KARANTA: Mutuwar wani Yaro a Kaduna ta harzuka matasa sun kone Coci, Caji Ofis da motocin jama’a kurmus
Yahanasu wanda ta bayyana cewar shekaru biyar kenan da aurensu, kuma suna da yaro guda daya, ta kara da cewa Nasiru baya kulawa da ita gaba daya, inda tace bai san cinta ba, bai san shanta ba, inji rahoton majiyar Legit.ng.
“Kunga dai Mijina baya Sallah, kuma baya bani abinci, ko magani idan nayi rashin lafiya baya bani.” Inji ta. Sai dai ta yi karin haske game da silar matsalar, inda tace tun bayan da suka samu wata sa-in-sa ne ta koma gidan iyayenta, watanni takwas kenan tana gida, shi kuma yayi watsi da ita.
Ta kara da cewa duk da tayi rashin lafiya, wanda yayi sanadiyar kwantar da ita a Asibiti, mijinta bai neme ta ba, balle ma ya biya kudin jinyar da tayi, don haka ne ta roki Kotun ta raba aurenta da shi, don kuwa ba zata iya zama da shi ba.
Sai dai gogan naku Nasiru ya musanta zarge zargen da matar ta yi masa, inda yace karya kawai ta ke yi masa, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.
Bayan sauraron dukkan bangarorin biyu, sai Alkali Musa Sa’ad ya dage sauraron karar zuwa 27 ga watan Maris, inda ya bukaci ma’auratan su kawo masa iyayensu da kuma shaidunsu, kafin ya yanke hukunci.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng