Mutuwar wani Yaro a Kaduna ta harzuka matasa sun kone Coci, Caji Ofis da motocin jama’a kurmus
Wani rikici da ya faru a jihar Kaduna a daren Talata, 20 ga watan Maris, ya bar baya da kura, inda a yanzu haka ake zaman dar dar unguwar da wannan lamari ya auku, inji rahoton Leadership.
Rikicin ya faru ne a unguwar bayan Dutse dake cikin karamar hukumar Chikun, inda wasu fusatattun matasa suka babbaka wano Cocin mabiya darikar Sele na addinin Kirista sakamakon zargin Faston cocin da kashe wani Yaro mai suna Sylvester saboda tsafi.
KU KARANTA: Bincike: An gano wani yaro guda daya daga cikin yan matan Dapchi da yan Boko Haram suka sako
Majiyar Legit.ng ta ruwaito koda Yansandan Narayi suka yi kokarin shiga lamarin sai matasan suka ce “Da wa Allah ya hada mu ba in ba ku ba” suka far musu, har sai da suka kona ofishin Yansandan dake unguwar Narayi.
Rahotanni sun bayyana cewar yaron mai shekaru 20 yana ma Faston cocin lebura ne a wani gini da yake yi a cikin wani rafi dake gefen cocin, inda yana cikin aikin ne sai kwatsa ya tunjuma cikin rafin, daga nan kuma yace ga garinku nan.
Nan da nan aka ce Faston ya ruga ofishin Yansandan Nariya, inda ya kai karar abinda ya faru, sai dai ko da matasan unguwar suka samu wannan labara, sai suka yi zargin Fastin yayi amfani da yaron ne wajen tsafe tsafe, ba tare da wata wata ba suka diran ma cocin, inda suka kone ta, tare da motar wani dan cocin, sa’annan suka ci gaba da zanga zanga suna bukatar a basu Faston dake hannun Yansandan Barnawa.
Amma dayake abin gama ya gama, tuni aka birne Sylvester da misalin karfe 10 na daren Talata, a nan gefen rafin daya mutu a ciki a karkashin jagorancin Faston Cocin ECWA, Mark Ayuba, wanda ya shawarce jama’a da kada su dauki doka a hannunsu.
Da aka tuntubi rundunar Yansandan jihar, Kaakakin rundunar ASP Mukhtar Aliyu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace Faston na hannunsu, kuma sun gana da shuwagabannin unguwar da nufi zakulo duk masu hannu cikin rikicin don hukunta su.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng