Yan sanda sun kashe mai garkuwa da mutane a Edo
Rundunar yan sandan jihar Edo sun kashe wani mai garkuwa da mutane a lokacin wani musayar wuta a Benin, babban birnin jihar Edo.
Da yake jawabi ga manema labarai a Benin, kwamishina yan sandan jihar, Babatunde Johnson Kokumo yace yan sanda sun kashe dan ta’addan ne a safiyar jiya, Talata , 21 ga watan Maris.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa da farko masu garkuwa su hudu sun sace wani Odion yayinda yake shiga gidansa a hanyar Sapele, Benin.
“Da muka samu labarin sace Odion sai muka bi sahun yan ta’addan sannan kuma a lokacin da jami’anmu sukayi kusa da su da safe a yankin Ugbo dake Benin, sai suka yi musayar wuta sannan aka kashe daya daga cikinsu yayinda uku suka gudu,” inji shi.
KU KARANTA KUMA: Darasin da muka koya daga mutuwar Wakili - Sanatoci
Da yake Magana da manema labarai, wanda abun ya cika da shi ya bayyana cewa masu garkuwan sun kama shi da bindiga da adduna sannan suka bukaci ya basu kudi.
Ya ce, “Lokacin da nace masu bani da kudi, sai suka umarce ni da na fito daga mota sannan suka tafi dani. Sun karbi yan kudaden dake jikina da kuma katin ATM. Sun kai ni wani kango.”
A baya Legit.ng ta kawo cewa wata babban kotun jihar Cross River ta yanke ma wani mutumi, Godwin Elewana wanda yayi ritaya daga kamfanin man Najeriya hukuncin kisa ta hanyar rataya kan kashe saurayin yarsa.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta: Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng