Wani dan neman maza da lalata kananan yara ya shiga hannun hukuma a jihar Legas

Wani dan neman maza da lalata kananan yara ya shiga hannun hukuma a jihar Legas

Wani direban mota dan shekara 42, Seyi Oluwukere, ya shiga hannun hukumar 'yan sanda a jihar Legas da laifin lalata da wani karamin yaro inda ya kuma ce ya aikata hakan wasu mutane bakwai daban da suka hadar har da manya.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, wannan malalaci dai ya yaudari karamin yaron ne tun daga filin su na buga kwallo har zuwa dakin sa dake kan hanyar Marshal ta unguwar Surulere a jihar Legas inda ya aikata wannan alfasha.

Jami'an 'yan sanda a bakin aiki
Jami'an 'yan sanda a bakin aiki

A cewar wannan karamin yaro dan shekara 12 da ba a bayyana sunan sa ba, "Mista Seyi dai ya janye shi daga filin wasa tare har zuwa dakin sa a bisa yaudara ta alkawarin taimakon sa da zai yi a harkar waka kasancewar sa mawaki."

"Zuwan su dakin ke da wuya, Seyi ya kwale kayan sa kuma ya umarci yaron da ya aikata kuma ya yi ba tare da wata kyuya ba, inda ya zakke ma sa ta dubura."

Wannan lamari ya sanya yaron ya gaza samun sukuni da har ya sanya ya labartawa iyayen sa halin da ya ciki inda su ka danganta lamarin ga hukumar 'yan sanda.

KARANTA KUMA: Majalisar Wakilai ta sake hurawa Buhari wuta kan dokar sauya jadawalin zabe da kafa hukumar Peace Corps

A yayin da Mista Seyi ya shiga hannun hukuma, ya shida ma su cewa wannan ba shine karo na farko da ya aikata wannan ta'asa ba, domin kuwa wannan yaro shine mutum na takwas da ya biya bukatar sa da shi.

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar Chike Oti, ya tabbatar da wannan lamari inda ya ce tuni bincike ya kankama domin gurfanar da direban a gaban kuliya.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, majalisar wakilai ta sake hurawa shugaban kasa Muhammadu Buhari wuta kan sauya jadawalin zabe da kafa hukumar Peace Corps cikin dokar kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng