Kotu tayi watsi da maganar tsige Yahaya Bello daga kujerar Gwamna

Kotu tayi watsi da maganar tsige Yahaya Bello daga kujerar Gwamna

- An nemi Kotu ta cire Yahaya Bello daga matsayin Gwamnan Kogi

- Kotu dai tace ba ta da hurumin shiga abin da ya faru kafin ayi zabe

- Bello ya hau mulki ne bayan babban ‘Dan takara a zaben ya mutu

Babban Kotun Tarayya da ke zama a Birnin Tarayya Abuja yayi watsi da karar da aka kawo gaban sa da yunkurin cire Gwamnan Jihar Kogi Alhaji Yahaya Bello daga ofis a makon nan. Bello ya samu hawa mulki ne bayan rasuwar Abubakar Audu.

Kotu tayi watsi da maganar tsige Yahaya Bello daga kujerar Gwamna
Bello ya zama Gwamna bayan Audu ya rasu ana cikin zabe

Alkali mai shari’a John Tsoho a Ranar Talata yayi facali da karar da ake yi na sauke Gwamna Yahaya Bello daga kujerar Gwamna. Alkali Tsoho yace Lauyoyin da su ka shigar da kara ba su da ta cewa a kan maganar kujerar Gwamnan.

KU KARANTA: Jami'an DSS sun yi awon-gaba da wani 'Dan a-mutun Kwankwaso

Kotu tayi watsi da maganar tsige Yahaya Bello daga kujerar Gwamna
An yi yunkurin sauke Gwamna Bello daga kujerar sa

Manyan Lauyoyin kasar nan Michael Elokun, Ibrahim Sule da kuma Hauwa Audi sun nemi Kotu ta tsige Yahaya Bello tayi maza ta maida tsohon Gwamna Idris Wada kan kujerar sa. Kotu dai ba ta ga dalilin yin wannan ba a zaman da tayi a Ranar Talatan nan.

Alkalin yace wadanda su ka shigar da karar ba ‘Ya ‘yan APC mai mulki bane kuma ba su yi takara a zaben na Gwamnan Jihar Kogi ba don haka babu dalilin zuwa Kotu. Asali ma dai Alkalin yace wannan matsala ce ta fitar da gwani Jam'iyya ba zabe ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng