Abubuwan da za su sa ‘Dan wasa Neymar ya tattara ya bar PSG

Abubuwan da za su sa ‘Dan wasa Neymar ya tattara ya bar PSG

Mun kawo wasu manyan dalilai da Jaridar Metro ta Kasar Ingila ta kawo da su ka sa babban ‘Dan wasan Duniya watau Neymar Jr. ya ke so ya tattara kayan sa daga PSG ya koma taka leda a Kungiyar Real Madrid nan da kakar bana.

A shekarar bara ne Neymar Jr. ya bar Barcelona inda ya koma Birnin Faris bayan Kungiyar PSG ta kashe sama da fam miliyan €220 a kan shi. Tuni dai har ‘Dan wasan ya nuna kwarewar sa amma fa yana neman tashi daga Faransa.

Abubuwan da za su sa ‘Dan wasa Neymar ya tattara ya bar PSG

Neymar Jr. na neman komawa bugawa Real Madrid

1. Keta daga ‘yan adawa

Daga cikin manyan dalilan da su ka sa Neymar ya ke neman barin PSG ya koma RealMadrid shi ne yawan ketan da ake yi masa a filin wasa inda su na karawa da wasu kulob din.

2. Yanayin busa wasa

Bayan irin ketar da ake yi wa ‘Dan wasan, Neymar yana kuka da yadda Alkalan wasa ke yin huri a kasar Faransa. Tauraron ‘Dan wasan yana ganin ba ayi masa adalci a filin kwallo.

KU KARANTA: Yaran da aka sace a Najeriya za su gana da Shugaban kasa

3. Rashin abokan hamayya

Yanzu dai kusan ka iya cewa Kungiyar PSG ta ci Gasar kofin gida ta gama don tuni ta dare saman tebur da maki 14. A Faransa dai an rasa wanda za su takawa kulob din su Neymar burki.

4. Filin kwallo

Haka kuma ‘Dan wasan na yawan kokawa da irin filayen wasan kasar Faransa inda yake ganin da dama ba su da kyau kuma za su rika ja yana samun rauni a wajen wasa.

5. Rashin yawo a jirgi

Har wa yau, Jaridar Metro ta rahoto cewa ‘Dan wasan bai jin dadin yadda Kungiyar sa ke yawan yawo zuwa wasa a mota maimakon a nemi jirgin sama ko kasa. Kuma dai bai jin dadin yadda Kocin Kungiyar Unai Emery yake tafiyar da abubuwa a Kulob din.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel