Gwamnan jihar Kaduna ya sanya tubalin gina gidaje 600 masu rangwame a jihar Kaduna (Hotuna)
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya kaddamar da fara ginin wasu gidaje guda 600 a jihar Kaduna masu rangwame, inda ya sanya tubalin ginin a ranar Laraba 21 ga watan Maris.
Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito an gudanar da taron sanya tubalin gidajen ne a unguwar Millenium City na jihar Kaduna, gine ginen da suka kunshi gidaje 600, da katafaren shagon siyayya.
KU KARANTA:Da sauran rina a kaba: Boko Haram sun ki sako wata dalibar daga cikin yan matan Dapchi, karanta dalilinsu
Majiyar Legit.ng ta ruwaito za ayi wannan gine gine ne da hadin gwiwa tsakanin hukumar bunkasa kasuwanci ta jihar Kaduna, KADIPA da kuma wasu kamfanonin yan kasuwa da suka hada da Nurus-Siraj da zasu gina gidaje 500, Ummhi Nigeria masu gidaje 100, sai kuma, Kamfanin Jifatu.
A yayin taron gwamna El-Rufai ya bayyana cewar gwamnatin jihar zata samar da ruwan famfo, wutar lantarki da kuma tsaro a unguwannin da ake gina gidajen, sa’annan ya bukaci jama’an unguwannin dasu baiwa kamfanonin hadin kai don ayi aiki tare da su.
“Ina fatan zamu dawo nan da shekara daya don kaddamar da kammala gaikin ginin idajen nan, dama an sanar damu cewar za’a kammala gina katafare shagon nan a watan Yuni.” Inji El-Rufai
Da take nata jawabin, shugaban hukumar KADIPA, Umma Aboki ta bayyana cewa a gwamnati na da yakinin kamfanoni masu gine gine zasu samar da gidajen da suka kai 3000 a cikin shekaru biyar masu zuwa.
Haka zalika ta tabbatar da manufar KADIPA na hada karfi da karfe da yan kasuwa don inganta kasuwanci a jiha Kaduna ta hanyar samar da shagunan zamani akan tsari, tare da samar musu da yanayi mai kyau don bunkasa kasuwancisu.
Bugu da kari bayan wannan bikin sanya tubali, gwamnan ya kara halartar taron sanya tubalin gina Otal da wajen shakatawa a bayan dandalin Murtala dake cikin garin Kaduna, wanda kamfanin AMSALCO ke ginawa.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng