Majalisar Wakilai ta sake hurawa Buhari wuta kan dokar sauya jadawalin zabe da kafa hukumar Peace Corps
A zaman majalisar wakilai da aka gudanar na ranar yau Laraba, ta sake sabunta bukatar ta ga shugaban kasa Muhammadu Buhari na neman amincewar akan sanya hukumar Nigerian Peace Corps cikin dokar kasa.
Majalisar ta kuma sake neman shugaba Buhari akan ya amince da dokar sauya jadawalin zabe na 2019.
A baya dai shugaban kasa yayi watsi tare da nuna rashin amincewar sa da wannan dokoki biyu, inda yake ganin sauya dokar zabe zai ci karo da tanadi na kundin tsari da ya baiwa hukumar zabe ta kasa watau INEC dama ta tsara duk wani fasali da kuma jadawalin zabe.
A yayin da shugaban ya kuma bayar da dalilin cewa, sanya hukumar Peace Corps cikin doka zai zamto maimai ga aikace-aikacen da wasu hukumomin tsaro ke gudanarwa a kasar nan.
Legit.ng ta fahimci cewa, wannan su ne manyan dalilai biyu da shugaban kasa ya bayar wajen yin watsi da bukatar majalisar tarayya da mambobin ke hankoron assasawa.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, majalisar ta kuma sake sabunta gabatar da bukatun ta ga shugaban kasa na neman amincewar sanya wasu sabbin dokoki da suka hadar har da kafa sabuwar jami'ar gwamnatin tarayya a garin Wukari.
KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya bayar da lamunin bashin $15bn domin ginin layin dogo daga Fatakwal zuwa Maiduguri
Rahotanni sun bayyana cewa, a yayin da wasu mambobin majalisar ke goyon bayan sanya wannan bukatu cikin dokar kasa, wasun su ko sun juya baya ga hakan inda suke goyon bayan shugaba Buhari.
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, kungiyar Jama'atu Nasril Islam ta yabawa gwamnatin tarayya kan kwazon ta na ceto wasu daga cikin 'yan Matan Dapchi da 'yan Boko Haram suka yi garkuwa da su a makonni da suka shude.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng