Hijab : Wani mallamin addini yayi kira da gwamnatin tarayya ta tabbatar da kare hakkokin musulmi a Najeriya
- Limamnin masalcin Garki yayi kira da gwamnatin tarayya ta tabbatar da kare hakkokin musulmi a Najeriya
- Sheikh Yahya Al-Yolawi ya bayyana damuwar sa akan yadda ake cin zarafin mata masu sanya hijabi a Najeriya
Wani Bbbbabn mallamin addinin musulunci mazaunin garin Abuja, Sheikh Yahya Al-Yolawi, yayi kira da gwamnatin tarayya ta tabbatar da kare hakokin musulmai a kasar
Shehin Mallamin, yayi wannan kira a wata hira da yayi da majiya jaridar News Agency of Nigeria (NAN) a ranar Laraba.
Sheikh Yahya Al-Yolawi shine limamin babban masallacin Area 10, dake Garki Abuja.
Yace, ya zama dole gwamnati tarayya ta hana cin zarafin matan dake sanya hijabi a fadin kasar, saboda sanya hijab wajibi ne ga mata a adinin musulunci.
KU KARANTA : Fusatattun matasa sun kona barawon waya a jihar Nasarawa
Mallamin ya bayyana damuwar sa akan yadda cin zarafi mata masu sanya hijabi a kasar ya zama ruwan dare
“Ya zama dole shugabanin musulmai su tashi tsaye su kare hakokin musulmai a cikin kasar nan," inji Sheikh Yahya Al-Yolawi.
Dannan wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng