Hukumar JAMB ta rike sakamako 111, 981 na jarrabawar dalibai
A wani sabon rahoto da hukumar JAMB ta fitar a ranar da ta gabata ya bayyana cewa, hukumar ta rike sakamako 111, 981 na jarrabawar wasu dalibai menama shiga jami'o'i a sanadiyar shakku da kuma tantama da sai ta tsananta bincike.
Mai magana da yawun hukumar Dakta Fabian Benjamin shine ya bayyana hakan da cewa, a sakamakon binciken na'uro'ri ma su daukar hoto da hukumar ta yi amfani da su wajen gudanar da jarrabawar ya sanya ta rike sakamakon wasu dalibai.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, hukumar ta saki sakamakon jarrabawa 1, 502,978 na dalibai manema shiga jami'o'i da kwalejai a fadin kasar nan. Sai dai har yanzu akwai sakamako 111, 981 da hukumar za ta tantance.
KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya shiga ganawa da tsohon mataimakin shugaban kasa, Namadi Sambo
Hukumar ta kuma bayyana cewa, kimanin dalibai 1, 652,825 suka yi rajistar jarrabawar ta neman shiga jami'o'i a wannan shekara 2018.
Legit.ng ta ruwaito cewa, Marigayi Sanata Wakil ya nemi uwargidan sa ta kawo ma sa Shayi kafin ajali ya katse ma sa hanzari.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng