Karshen alewa ƙasa: Matasa sun kama wani ɓarawo da yayi garkuwa da yan mata guda 2 a Kaduna

Karshen alewa ƙasa: Matasa sun kama wani ɓarawo da yayi garkuwa da yan mata guda 2 a Kaduna

Wasu jaruman matasan unguwar Hayin Rigasa dake cikin karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna sun yi nasarar cafke wani kasurgumin baarwon mutane da ya shahara wajen yin garkuwa da mutane kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Da fari dai majiyar Legit.ng ta ruwaito wasu masu garkuwa da mutane a jihar Kaduna sun saci wasu yan mata guda biyu yan gida daya, a unguwarsu dake can kusa da sabuwar tashar jirgin kasa dake unguwar Rigasa.

KU KARANTA: Wasu gagararrun yan fashi da makami guda 4 sun fada komar Yansandan jihar Kano

Mahaifin yan matan malam Halliru ya bayyana cewa matasan unguwar ne suka yi ta maza, inda suka bi diddigin inda za’a biya masu garkuwa da mutanen kudin fansa kamar yadda suka nema, inda a lokacin da daya daga cikinsu yazo daukan kudin ne suka daka masa wawa.

Karshen alewa ƙasa: Matasa sun kama wani ɓarawo da yayi garkuwa da yan mata guda 2 a Kaduna
Yan matan

Majiyar mu ta tattauna da yan matan, inda suka shaida mata cewar da misalin karfe 2 na daren wata lahadi ne barayin suka afka cikin gidansu, yayin da suke barci, inda suka bukaci a basu kudi da wayoyi.

“Da suka tambayi mahaifinmu ya basu kudi, shi kuma yace bashi da kudi, hakan ta sa suka kwashe mu, suka yi awon gaba damu tare da fada masa cewa a duk lokacin da ya basu kudin da suka nema, zasu sako mu.” Inji yan matan.

Sai dai yan matan sun tabbatar da cewar barayin sun yi musu fyade, bayan nan suka lakada musun dan banzan duka, sa’annan suka jefa cikin wani ramu, inda a nan suka kwana. Daga karshe suka nemi a biyasu kudin fansa naira miliyan 1.

Dayake tattaunawa da majiyarmu, Malam Halliru ya bayyana cewa ya bukaci yayan nasa su dauki wannan al’amari da ya faru dasu a matsayin wata jarabawa daga Allah, don haka su yi hakuri. Sa’annan yace sai da ya je ya ajiye ma barayin naira miliyan daya a gindin wata bishiya kamar yadda suka bukata sa’annan suka sako masa yayansa.

“Amma a lokacin da suka turo daya daga cikinsu yazo ya dauki kudin ne, sai matasan unguwarmu suka yi masa kawanya, inda suka daka masa wawa, kuma yayan nawa sun gane shi.” Inji Mahaifinsu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng