An damke wani kasungumin dillalin bindigogi a Jihar Kaduna

An damke wani kasungumin dillalin bindigogi a Jihar Kaduna

- Dakarun Soji na Mobile Strike Team II da aka aike jihar Kaduna snyi nasarar kama wanni gawurtaccen dalilin bindiga

- Sojojin sun gano bindigogi kirar AK 47 guda 2 da kuma harsashi guda 38

- Dakarun Sojin suna aikin sintiri ne a dajin Rigachikun da wuraren da ke makwabtaka da yankin ne lokacin da sukayi kacibus dashi

Dakarun Sojin Najeriya na 'Mobile Strike Team II' da aka aike jihar Kaduna sunyi nasarar damke wani gaurtaccen dalilin bindiga kana sun gano bindigogi kirar AK 47 guda biyu tare da harsashai guda 38.

Tawagar sojojin sunyi nasarar damke dillalin bindigogin ne ranar Litinin 19 ga watan Maris a wata samame da suka kai cikin dajin Rigachikun inda ake tunanin bata gari na buya.

An damke wani kasungumin dillalin bindigogi a Kaduna
An damke wani kasungumin dillalin bindigogi a Kaduna

KU KARANTA: Allah ya yiwa shugaban makarantar sakandire mafi dadewa a aiki rasuwa

Legit.ng ta gano cewa Hukumar Sojin Najeriya ta sanya idannu sosai a yankin na Rigachikun da kewaye saboda yawaitar miyagun ayyuka da batagari keyi a yankin.

An damke wani kasungumin dillalin bindigogi a Kaduna
An damke wani kasungumin dillalin bindigogi a Kaduna

Wata sanarwa da directan hulda da al'umma na Hukumar Sojin Najeriya, Brigadier Janar Texas Chukwu ya aike wa Legit.ng ya bayyana cewa sojojin na Najeriya sun mamaye yankin saboda su ci galaban bata garin da suka yiwa yankin katutu.

"Nasarorin da Hukumar Sojin ta ke samu kwanakin nan ya faru saboda matakan da sojin suka dauka na mamaye yankin don zakulo dukkan miyagun da ke aikata laifuka da suka hada da garkuwa da mutane, fashi da makami da satan shanu," inji sanarwa

A kwanakin nan, dakarun sojin kwace makamai da dama a jihar Taraba bayan sun gudanar da bincike a garuruwan Kwesati da Tati da ke karamar hukumar Takum.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: