Ni nayi komai na bikin diya ta, har suyar cin-cin - Uwargida Dolapo Osinbajo

Ni nayi komai na bikin diya ta, har suyar cin-cin - Uwargida Dolapo Osinbajo

Uwargidan mataimakin shugaban kasa, Dolapo Osinbajo, ta bayyana cewar ita ta dauki dawainiyar dukkan wahalhalun cikin gida yayin bikin diyar ta, Oluwadamilola.

Uwargida Dolapo ta watsa hotunanta a dandalin sada zumunta na Instagram yayin da take gyaran cake din bikin diyar ta.

"Ina matukar alfahari da yiwa diya ta suyar cake din bikinta. Yana daga cikin tarbiyar da iyaye da kakanni su ka dora mu a kai," a cewar Dolapo.

A karshen satin da ya gabata ne aka daura auren diyar Osinbajo da sahibinta, dan tsohon sojan Najeriya, John Shagaya.

Ni nayi komai na bikin diya ta, har suyar cin-cin - Uwargida Dolapo Osinbajo
Ni nayi komai na bikin diya ta, har suyar cin-cin - Uwargida Dolapo Osinbajo

Manyan baki daga ciki da wajen Najeriya sun halarci taron bikin.

Shugaba Buhari da mai dakinsa, Aisha Buhari, da manyan jami'an gwamnatin tarayya da na jihohi sun harci liyafar bikin.

DUBA WANNAN: Sifeto janar ya bayar da umarnin janye jami'an 'yan sanda daga jikin shafaffu da mai

A wani labarin Legit.ng, kun ji cewar shugaban kwamitin shura na addinin musulunci a Najeriya, Sa'ad Abubakar III, ya bayyana yau, Litinin; 19 ga watan Maris, a matsayin ranar farko ta watan Rajab, hijira ta 1439AH.

Sanarwar na kunshe ne cikin wata takarda da shugaban kwamitin harkokin addinin Islama kuma wazirin sarkin Musulmi, Farfesa Sambo Wali, ya sanyawa hannu, tare da bayyana cewar sun fitar da sanarwar ne sabida da rashin samun rahotonton ganin sabon wata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng