Yan bindiga a kauyukan jihar Zamfara sun hallaka mutane 8 basu ji ba, basu gani ba
Hare haren yan bindiga a jihar Zamfara ya cigaba da ruruwa, inda was yan bindiga suka far ma kauyen Dogon Daji a cikin karamar hukumar Maru, inda suka hallaka akalla mutane takwas, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan harin ya faru ne kimanin sati biyu da kashe shugaban barayin shanu na jihar Zamfara, Buharin Daji, a hannun wani tsohon abokin aikinsa daya tuba, Dogo Gide.
KU KARANTA: Tazarce: Viladmir Putin ya zarce karo na 4 a matsayin shugaban kasar Rasha
Ko a satin daya gabata, sai da kimanin mutane 41 suka rasa rayukansu a kauyen Birane, a lokacin da wasu yan bindiga suka kai hari a karamar hukumar Zurmi.
Wani mazaunin kauyen, Yushau Bingi ya shaida ma majiyarmu cewar sun binne mutane 7, yayind a yan bindigan suka yi awon gaba da wasu mutanen garin, hakazalika shima tsohon kansilan mazabar Bingi, Musa Umar ya tabbatar da kisan mutane takwas a yayin a harin.
Musa Umar ya bayyana cewar tun bayan kisan da aka yi ma Buharin Daji, yan bindiga sun yi ta karkasge mutane kamar kiyashi, inda yace a yan kwanakin nan ma sai da suka kashe yaronsa, suka kuma babbaka gawarsa, haka zalika sun kai hare hare a kauyen Dan Marke, da sauran ire iren hare haren nan.
Sai dai kwamishinan Yansandan jihar, Mista Kenneth Ebrimson ya bayyana cewa tuni sun aika da jami’ansu zuwa kauyen don tabbatar da tsaron dukiya da rayukan jama’an yankin.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng