Gwamnatin jihar Kano zata kashe naira biliyan N4bn wajen gina gada da wasu hanyoyi
- Gwamna Ganduje ya amince da kashe naira N4bn wajen gina gada da wasu hanyoyi a jihar Kano
- Gada da gwamnatin jiahr Kano zata gina zai dauki tsawon watanni bakwai
Gwamnatin jihar Kano ta amince da ware na biliyan N4bn dan gina sabuwar gada da zai hada hanyar Zarai Road, Silver Jubilee, Zoo Road zuwa cikin garin Kano.
Aikin da gwamatin jihar Kano zata kadamar zai hada da gadar kasa dake akan titin Zaria, sai kuma gadar zata taso daga kan titin Gidan Zoo ta sauka a gefen Massallacin Aliyu Ibn Abu Talib.
Kwamsihinan watsa labaru da al’adu na jihar Kano, Malam Muhammad Garba, ya bayyana haka a wata taro da ya halarta a birnin Abuja.
KU KARANTA : Mamora yaki karban sabuwar mukamin da Buhari ya bashi
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya amince da a fara aikin a taron majalissar zartarwar karo 11 na jihar Kano da ya jagoranta.
Wannan aiki dai za’a gina shi ne akan kudi N4Billion kuma ana sa ran fara shi a wannan watan Maris, sannan a kammala shi watan okotoba na cikin wannan shekara.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng