Majalisa ta dauki tsattsauran mataki kan lemun Fanta da Sprite

Majalisa ta dauki tsattsauran mataki kan lemun Fanta da Sprite

- ‘Yan Majalisa sun nemi kamfanin Coca-cola su canza salon su a Najeriya

- An yi kira ga kamfanin su bayyana sunayen duk sinadaran da su ke sa wa

- Akwai wasu sinadaran da ba su da amfani ko ma su ke da illa ga Bil Adama

Kwanakin baya aka yi ta surutu game da sinadaran da ke cikin lemun Fanta da Sprite. Yanzu dai ‘Yan Majalisar Kasar sun gindaya kamfanin na Coca-Cola da ke wannan lemu wasu sharadi. An kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta kara tashi tsaye.

Majalisa ta dauki tsattsauran mataki kan lemun Fanta da Sprite
Akwai irin su Benzoic acid a cikin lemun Fanta

Da farko dai an nemi Hukumar NAFDAC da ke kula da magunguna da abin ci da sha a Najeriya su tursasawa kamfuna su bayyana sinadaran da ke cikin lemun na su. A cikin sinadaran dai akwai wanda zai iya bada matsala idan aka sha da Bitamin C.

KU KARANTA: Sankarau ta kashe jama'a a cikin Jihar Katsina

‘Yan Majalisar Tarayya sun nemi masu yin lemun a Najeriya su gargadi duk wanda ya saye kayan su ta hanyar bayyana sunayen irin abubuwan da yake kwankwada. Wannan dai zai sa jama’a su cire shakka sannan kuma an yi adalci wajen kasuwanci.

Shugaban masu rinjaye a Majalisar Femi Gbajiamilla yayi bincike game da wannan lamarin inda jama’a su koka da cewa akwai abubuwa masu illa a lemun Fanta da Sprite. Masu yin lemun kan sa wasu sinadaran fiye da kima a lemun kasar nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng