Idan ba mu yi da gaske ba Jam’iyyar PDP za ta mutu - Orubebe

Idan ba mu yi da gaske ba Jam’iyyar PDP za ta mutu - Orubebe

- Wani tsohon Ministan Neja-Delta ya rubutawa Shugaban PDP wasika

- Orubebe ya bayyana inda Jam’iyyar tayi sakaci da kuma hanyar gyara

- Godwin Orubebe yace dole Jam’iyyar PDP ta samu hanyar kudin shiga

Mun samu labari daga Jaridar The Nation cewa tsohon Ministan Neja-Delta a lokacin Shugaban kasa Goodluck Jonathan yayi kaca-kaca da Jam’iyyar PDP a wata takarda da ya aika inda yace yanzu Jam’iyyar ta kama layin bata.

Idan ba mu yi da gaske ba Jam’iyyar PDP za ta mutu - Orubebe
Tsohon Ministan Neja-Delta yace Jam’iyyar PDP na cikin matsala

Godwin Elder Orubebe yayi kira ga Jam’iyyar PDP da su yi maza su kama shirin gyara idan ba haka ba kuwa Jam’iyyar za ta shiga cikin littatafan tarihi. Orubebe yace har yanzu Jam’iyyar PDP ba ta cikin hayyacin ta tun zaben 2015.

KU KARANTA: Assha: An kunyatar da Gwamnan Jihar Jigawa Badaru

Tsohon Ministan ya koka a wata wasika da ya rubutawa Shugaban Jam’iyyar da yadda zari da kama-karya da kuma girman kan wasu ya sa Jam’iyyar ta sha kashi a 2015 musamman a wajen taron gangamin da ta shirya na karshe a lokacin.

Mista Orubebe yace dole PDP ta yarda cewa tayi kuskure lokacin da tayi mulki. A cewar tsohon Ministan, gajiyawar Jam’iyyar ta sa Obasanjo ke kokarin kafa wata Kungiya. Orubebe ya kuma nemi PDP ta nemi kudi gudun kar wasu daidaiku su saye Jam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng