Sauran kiris: Hukumar soji ta fadi lokacin da zata kubutar da 'yan matan Dapchi

Sauran kiris: Hukumar soji ta fadi lokacin da zata kubutar da 'yan matan Dapchi

- 'Yan mata 110 mayakan kungiyar Boko Haram su ka sace daga makarantar sakandiren 'yan mata dake garin Dapchi a jihar Yobe

- Hukumar sojin Najeriya na cigaba da farautar mayakan kungiyar Boko Haram domin ceto 'yan matan

- Ministan tsaro, Mansur Dan-Ali, ya ce, cikin sati daya ko biyu ma su zuwa, dakarun soji zasu kubutar da 'yan matan

Ministan tsaron Najeriya, Mansur Dan-Ali, ya bayar da tabbacin cewar cikin sati daya ko biyu dakarun soji zasu kubutar da 'yan matan Dapchi da mayakan kungiyar Boko Haram su ka sace.

Ministan ya bayar da wannan tabbacin ne a jiya Asabar yayin da ya bayyana a wani shirin gidan talabijin na Channels.

Sauran kiris: Hukumar soji ta fadi lokacin da zata kubutar da 'yan matan Dapchi
Ministan tsaro; Mansur Dan-Ali

Dan-Ali ya ce, "Muna daf da kubutar da 'yan matan na Dapchi da mayakan kungiyar Boko Haram su ka sace. Mai yiwuwa cikin sati daya, zai iya kasance sati biyu, amma nan bada dadewa ba 'yan matan zasu samu 'yancinsu."

DUBA WANNAN: An yi barin wuta tsakanin dakarun soji da wasu 'yan bindiga a jihar Bauchi

A ranar 19 ga watan Fabrairu ne mayakan kungiyar Boko Haram su ka wani harin bazata makarantar sakandiren 'yan mata dake Dapchi a jihar Yobe tare da yin awon gaba da 'yan mata 110.

Dan-Ali ya bayar da tabbacin cewar 'yan matan zasu dawo gida kwanannan tare da bayyana cewar gwamnatin na bin dukkan matakan da su ka dace domin ganin hakan ta tabbata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng