An yi barin wuta tsakanin dakarun soji da wasu 'yan bindiga a jihar Bauchi
- Dakarun soji da wasu 'yan bindiga sun yi musayar wuta da tsakar rana a jiya juma'a a karamar hukumar Ningi ta jihar Bauchi
- Dakarun soji sun kashe 'yan bindigar hudu tare da kwace makamai
- Hukumar soji ta bukaci jama'a da su samar da bayanai masu muhimmanci gareta
Dakarun sojin Najeriya, na runduna ta 33 dake aikin tabbatar da zaman lafiya mai taken Ofireshon Lafiya Dole, ta yi arangama da wasu 'yan bindiga a jiya a daidai kan kwanar Burra dake karamar hukumar Ningi a jihar Bauchi.
Darektan yada labarai na hukumar sojin, Janar Texas Chukwu, ya bayyana cewar jami'an sojin sun fita aikin sintiri ne yayin da su ka yi kacibus da 'yan bindigar da misalin karfe 12:30 na rana.
'Yan bindigar sun bude wuta a kan tawagar sojin kuma ba tare da jinkiri ba su ka mayar da martani ga 'yan bindigar.
Bayan fafatawa da musayar wuta ta tsawon lokaci, dakarun sojin sun yi nasarar kashe hudu daga cikin 'yan bindigar tare da kwace wasu bindigu 5, babura 38, da kekuna 9, daga wurinsu.
DUBA WANNAN: Hakimi ya raunata mutum biyu tare da kashe daya daga cikin wadanda su ka yi kokarin sace shi
Kazalika an kama tara daga cikin 'yan bindigar a yayin da jami'in soji da ya samu rauni sakamakon musayar wuta aka garzaya da shi asibiti inda yanzu haka yake murmurewa.
Hukumar sojin ta ce tana cigaba da farautar 'yan bindigar da su ka tsere tare da bukatar jama'a su samar da rundunar sojin da bayanai ma su muhimmanci.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng