Cikin Hotuna: Ganduje zai kammala ayyukan da gwamnatin Kwankwaso ta gaza a jihar Kano
Da sanadin babban hadimi na musamman ga gwamnatin jihar Kano akan sabuwar hanyar sadarwa, Salihu Tanko Yakasai, mun samu rahoton cewa gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai yiwa gazawar Kwankwaso wankin babban bargo.
Hadimin ya bayyana cewa, Gwamna Ganduje zai kammala wannan sanbaleliyar gadar nan ta Sabon Gari mai tsawon kilomita 2 da tsohuwar gwamnatin Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso tayi watsi da ita.
KARANTA KUMA: Wani dan shekara 29 ya fyade mai juna biyu har cikin gidan ta na aure a garin Legas
Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnatin Kwankwaso ko kashi 20 cikin 100 na aikin gadar ba ta aiwatar ba, wanda a yanzu ake san ran Khadimul Islama zai kammala ta zuwa watan Agusta na shekarar nan ta 2018 sakamakon kashi 80 da ake a halin yanzu wajen aiwatar da ita.
Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wani mai karancin kunya ya yiwa mai juna biyu aika-aika har cikin gidan ta na aure a jihar Legas.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng