Dan sanda ya far wa kwamandan Peace Corp bayan ya kwace ma wani jami'in hukumar kayan aikin sa

Dan sanda ya far wa kwamandan Peace Corp bayan ya kwace ma wani jami'in hukumar kayan aikin sa

- Kwamandan jami'in hukumar Peace Corp ya yi ikirarin cewa wani jami'in Dan sanda ya ci mutuncinsa

- Ya ce Dan sandan ya tare shi wani jami'in Peace Corps a hanya kuma ya kwace masa hula da damara kana ya tsare shi

- Daga bisani bayan da kwamandan ya biyo jin ba'asi, Dan sanda ya ci ma kwala kuma ya yi barazanar harbin sa da bindiga

An zargi jami'in dan Sanda, Sajan Oluwole Oke, da laifin cin mutuncin kwamandan Jiha na Peace Corps, na jihar Osun, Mr Paul Ayinde, bayan sun karbe masa kayan aikinsa.

Kwamandan ya fadawa dan jaridar Punch wayar salula, ranar Juma’a, cewa daya daga cikin jami'an sa na tuki kan hanyar Ede-Ife, lokacin da jami’an ‘Yan Sanda sauka tsayar dashi a kauyen Agbungu.

'Yan sanda sun ragargaji kwamandan Peace Corps, sun kwace masa uniform
'Yan sanda sun ragargaji kwamandan Peace Corps, sun kwace masa uniform

KU KARANTA: Diya ta na sha'awar sarautar Kano idan na gama, inji Sarki Sanusi

Yace, sun bukaci ma’aikacin Peace Corps din ya nuna masu takardun motarsa, ya kuma yi masu bayanin kowanene shi, inda yayi kamar yanda suka umurta, amma hakan bai hana Oke ya cire masa hula ya kuma karbe masa damara ba, yace masa bashi da hurumin sanya kayan aikin saboda Gwamnatin Tarayya bata amince da kafuwar su ba.

Bayan duk bayanai daya yiwa Jami’in ‘Yan Sandan wanda bai gamsu dashi ba ya cigaba da tsareshi har na tsawon sa’o’i biyu, kafin kwamandansu ya iso wurin.

Ayince ya ce bayan rokonsa a kan ya sallami ma’aikacin nawa, sai ya kirani da mara hankali, ya kuma rike wuyan rigata har ma ya yi mani barazana da Bindiga. Daya daga cikin ma’aikatana yayi kokarin dauka bidiyo da waya ta amma jam’in ya lalata wayar.

Da farko kwamandan yayi niyyar kai dan Sandan kara kotu, amma dai daga baya ya canja shawara. Sai dai ya yi kira ga shugaban hukumar ‘Yan Sanda na Jihar, wanda ya bayyana a matsayin “mutumin kirki” da ya fadakar da ma’aikatansa a kan Peace Corps.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164