Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi ta shirya addu’ar kwanaki 3 ga Najeriya

Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi ta shirya addu’ar kwanaki 3 ga Najeriya

- Gidauniyar ta Shaikh Dahiru Usman Bauchi tayi kira don yiwa Najeriya addu’ar kwanaki uku

- Gidauniyar za tayi hakan ne sakamakon matsaloli da ake fuskanta na tsaro a Najeriya

- Ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari, Sheikh Dahiru Usman Bauchi da wasu manyan baki za su hallarci taron addua'r

Gidauniyar Shaikh Dahiru Usman Bauchi tayi kira don yiwa Najeriya addu’ar kwanaki uku, daga 11 zuwa 14 ga watan Afirilun 2018, don neman taimakon Allah game da matsalolin tsaro da ake fuskanta a Najeriya.

Gidauniyar Shaikh Dahiru Bauchi ta shirya addu’ar kwanaki 3 ga Najeriya
Gidauniyar Shaikh Dahiru Bauchi ta shirya addu’ar kwanaki 3 ga Najeriya

Wannan sanarwan ta fito ne daga bakin shugaban gidauniyar, Sheikh Ibrahim Dahiru Usman Bauchi a wata hira ta ya yi da jaridar Leadership a ranar laraba 14 ga watan Maris na 2018. Ana sa ran Shugaba Muhammadu Buhari, da Sheikh Dahiru Usman Bauchi da kuma wasu manyan baki za su hallarci taron addua'ar da za'ayi a Abuja.

KU KARANTA: Diya ta na sha'awar sarautar Kano idan na gama, inji Sarki Sanusi

Gidauniyar za ta yi hakan ne, sakamakon matsaloli da ake fuskanta na tsaro a Najeriya, wanda suka hada da fadan manoma da makiyaya, kabilanci, addini, da dadan yanki, sannan ga yawan satar mutane da akeyi a fadin kasar nan.

Shugaban gidauniyar yace za’ayi addu’a, da nufin samun cigaba a kasa baki daya, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa, da manema labarai, a ranar Laraba, 14 ga watan Maris, 2018. Ya kara da cewa, Najeriya tana da matukar bukatar addu’a a wannan lokaci da take ciki.

Yace; “A musulunci ba wani makamin da yafi addu’a. Addu’a a koda yaushe itace abu na farko da mutum ya kamata yayi don neman tsari daga ko wane irin sharri".

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164