Mutane da dama sun mutu sakamakon barkewar rikici tsakanin Hausawa da Yarbawa a Legas

Mutane da dama sun mutu sakamakon barkewar rikici tsakanin Hausawa da Yarbawa a Legas

- Anyi wata kazamar karon batta tsakanin Hausawa da Yarbawa a Ojota dake garin Legas

- Rahotanni sun bayyana cewar rikicin ya yi sanadiyar mutuwar mutane da yawa

- Rikicin ya barke ne bayan wani Bahaushe ya lakadawa wani Bayarabe duka bayan saboda wani sabani da ya shiga tsakaninsu

Barkewar wani kazamin rikici tsakanin Hausawa da Yarabawa dake zaune a Gidan Panli dake tashar motar Ojota a garin Legas ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare jikkata wasu da yawa.

Jaridar Punch ya rawaito cewar rikicin mai nasaba da kabilanci ya barke ne ranar Alhamis, 15 ga watan Maris, bayan wani Bahaushe ya lakadawa wani Bayarabe dukan tsiya sakamakon wata rashin fahimta da ta shiga tsakaninsu.

Mutane da dama sun mutu sakamakon barkewar rikici tsakanin Hausawa da Yarbawa a Legas
Mutane da dama sun mutu sakamakon barkewar rikici tsakanin Hausawa da Yarbawa a Legas

Rahotanni sun bayyana cewar rikicin ya kara kazanta ne a yau juma'a bayan wasu gungun matasa 'yan kabilar Yoruba sun yiwa unguwar Hausawa tsinke domin daukar fansan dukan dan uwansu.

KU KARANTA: Daliban jami’ar Ahmadu Bello su kera matatan man fetur

Rikicin ya jawo dakatar da harkokin kasuwanci a yankin tare kone-konen ababen hawa.

Wani shaidar gani da ido, Ajayi, ya bayyanawa manema labarai cewar sabani tsakanin wasu matasa biyu; bahaushe da bayarabe, ya haddasa rikicin.

Ya kara da cewar, al'amura sun kara dagulewa ne bayan wasu matasa 'yan kabilar Yoruba sun kai harin fansa a kan Hausawa mazauna yankin na Ojota.

'Yan kasuwa sun rufe shagunan sana'o'insu tare da cika wandonsu da iska.

Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Legas, SP Chike Oti, ya tabbatar da cewar al'amura sun samu daidaito a yankin bayan zuwan jami'an tsaron sanda unguwar da rikicin ya shafa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164