Shuwagabannin Najeriya sun halarci auren ɗiyar hamshain attajiri Aliko Dangote, Fatima a jihar Kano

Shuwagabannin Najeriya sun halarci auren ɗiyar hamshain attajiri Aliko Dangote, Fatima a jihar Kano

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci taron daurin auren diyar fitacce kuma hamshakin attajirin nan Alhaji Aliko Dangote, wanda ya gudana a jihar Kano a ranar Juma’a 16 ga watan Maris.

Daily Trust ta ruwaito shugaba Buhari ne ya aurar da Fatima Dangote ga angonta Jamilu, yaron tsohon babban sufetan Yansandan Najeriya, M.D Abubakar a bisa sadaki N500,000.

KU KARANTA: Dogo Gide: Mutumin da ya yi ajalin Buharin Daji

Shuwagabannin Najeriya sun halarci auren ɗiyar hamshain attajiri Aliko Dangote, Fatima a jihar Kano
Auren

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mai martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sunusi ne ya daura wannan aure da ya samu halartar jiga jigan yan siyasa, hamshakan yan kasuwa, manyan jamian gwamnati tare da mai kudin Duniya, Bill Gates.

Dag cikin wadanda suka samu halartar taron akwai shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, Kaakakin majalisa Yakubu Dogara, tsohon shugaban kasa Abdulsalam Abubakar, Janar Aliyu Gusau, ministan sadarwa Adebayo Shitu.

Shuwagabannin Najeriya sun halarci auren ɗiyar hamshain attajiri Aliko Dangote, Fatima a jihar Kano
Auren

Daga bangaren gwamnoni kuwa, gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ne mai masaukin baki, kuma ya sauki gwamnan jihar Katsina Aminu Masari, na Sakkwato Aminu Tambuwal, na Nassarawa, Tanko Al-Makura, na Kwara Abdulfatah Ahmed.

Shuwagabannin Najeriya sun halarci auren ɗiyar hamshain attajiri Aliko Dangote, Fatima a jihar Kano
Auren

Sauran suna hada da Gwamnan Borno, Kashim shettima, na Yobe Ibrahim Geidam na Kogi Yahaya Bello, na Ogun Ibikunle Amosun na Oyo Abiola AJimobi da gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufai.

Shuwagabannin Najeriya sun halarci auren ɗiyar hamshain attajiri Aliko Dangote, Fatima a jihar Kano
Auren

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng