Wutar lantarki ta hallaka wani Barawon da yayi yunkurin satar Turansufoma sukutum a Kaduna
Jama’a na cewa duk wanda ya biye ma ransa yayi abinda take so, tabbas zai ga abinda baya so kuwa, kwatankwacin haka ne ta faru da wani matashi a jihar Kaduna mai budurwa zuciya.
Wannan lamari ya faru ne a unguwar Barnawa High cost dake cikin garin Kaduna, inda aka wayi gari aka tsinci gawar wani matashi a makale da na’urar rarraba wutar lantarki, wato turansfoma.
KU KARANTA: Soyayya: Yadda wata budurwa ta banka ma kanta wuta akan Saurayi a Jigawa
Daily Trust ta ruwaito jama’an unguwar na cewa suna zargin mutumin barawo ne, kuma yayi kokarin sace musu Turansfuma ne, ko kuma wani abu daga cikin Turansufomar, da ake sacewa ake siyawar.
Kamar yadda aka ga gawar mutumin, ta nuna cewar hawa yayi kan wasu manyan falwayoyin wuta guda biyu, wadanda suke dauke da na’urar turansufomar a can sama, inda barawon ya dare da nufin kwantota.
Daga bisani a safiyar Juma’a, an hangi jami’an hukumar wutar lantarki ta Kaduna, KAEDCO, sun isa wajen, inda suka bambabaro gawar barawon daga jikin karafan da ya makale da su a saman.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng