Wani jirgin sama cike da fasinjoji yayi saukar da bai shirya ba a Sokoto
- Wani jirgin sama na Aero ya samu matsala a kan hanyar Abuja
- Don dole jirgin ya sauka a Sokoto bayan da ya gaza shiga giya
- Kamfanin Aero ya maidawa fasinjojin kudin su su ka sake shiri
Jaridar The Cable ta rahoto cewa wani jirgin Aero yayi durar angulu gudun kar a samu matsala a filin jirgin sama na Sultan Abubakar III da ke Garin Sokoto. An dai shirya zuwa Abuja ne daga Sokoto amma tafiyar ba ta yiwu ba aka fasa.
Babban jirgin Boeing 737 na Kamfanin Aero yayi saukar da bai yi niyya ba a Garin Sokoto bayan ya samu matsalar giya a Ranar Laraba da ta wuce. Wadanda ke cikin jirgin sun ce an yi ta jin kara daga injin jirgin lokacin yana sama.
KU KARANTA: Za a dauki 'Yan Sanda 6000 aiki a Najeriya
Bayan an fara tafiya ne abin ya ki yiwuwa don haka Matukin jirgin dai ya sanar da cewa sun samu matsala don kuwa jirgin ya gagara shiga giya. Don dole dai ba ayi wata-wata ba aka sauka a Sokoto da kimanin karfe 3:00 na tsakar rana.
Bayan an sauko kasa an yi kokarin duba giyan jirgin amma abin ya faskara wanda dole ya sa aka canza tafiya aka nemi wani jirgin dabam. Allah dai yayi cikin fasinjojin babu wanda ya gamu da wata matsala sai dai aka maida masu kudin su.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng