Dubi jerin jihohin da ke kan gaba wajen ciyo bashi daga kasashen waje
- Jihar Legas da tafi kowa a bangaren tattalin arziki a Najeriya amma kuma itace kuma tafi kowa ciyo bashi daga kasashen waje
- Wasu takardu masu da ke kunshe da bayanan basusukan jihohin da na Gwamnatin Tarayya a watan Disamba, 2017’, ya nuna jihohin Kaduna, da Edo, suna cikin uku na fari a jerin
- Hakan na nuna cewa Gwamnatin Tarayya na rike da kashi 78.27 a cikin 100 na bashin waje, inda gwamnatocin jihohi kuma suna rike da sauran kashin
Jihar Legas da tafi kowa a bangaren tattalin arziki a Najeriya, itace kuma tafi kowa ciyo bashin kasashen waje, a tsakanin gwamnatocin jihohi dake cikin kasar nan, lissafin da aka samo daga Ofishin kula da bashi ya nuna.
Wasu takardu masu lakabi da ‘bayanai akan masu bashi a waje cikin gwamnatin Jiha da ta Tarayya a watan Disamba, 2017’, ya nuna jihohin Kaduna, da Edo suna cikin uku na fari a jerin sunayen wadanda suka fi cin bashi a daga kasashen waje.
KU KARANTA: An gurfanar da fasto bisa zargin mu'ujizar karya da ya yi amfani dashi don karbe motocin mambobin sa
Da bashin kasashen waje na $1.47bn, Legas ita kadai ce jihar mai bashin waje sama $1bn, a cikin basussukan jihar na $4.12 wanda wake binta a waje wanda ke kashi 35.68 cikin dari.
Jihar Kaduna na da bashin $238.28m, sai Jihar Edo, na da bashin $232.2m. Hakan na nuna cewa, Kaduna na rike da kashi 5.78 a cikin 100 na bashin kasashen waje, yayinda Edo, keda kashi 5.63 bisa 100 na bashin jihohi a waje.
A ranar 31, ga watan Disamba, 2017, bashin Najeriya na kasar waje ya kai $18.91bn. Daga wadanan, gwamnatin Tarayya tana da bashin $14.8m.
Duk da haka, bashin gida yana rinjaye akan bashin kasar, tare da asusun ajiyar gida na kimanin kashi 73 cikin dari, yayin da kasashen waje sun daidaita ma’auni na kashi 27 cikin dari na bashin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng