Sabbin kamfanin shinkafa 8 sun kai Najeriya wani mataki na son barka - Bagudu

Sabbin kamfanin shinkafa 8 sun kai Najeriya wani mataki na son barka - Bagudu

Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya bayyana cewa, Najeriya ta fara kafa tuta wajen wadatar shinkafa yayin da samun wannan hatsi ya haura daga tan miliyan 5.7 zuwa tan miliyan 17 cikin shekaru biyu da rabi kacal da suka gabata.

Gwamnan ya bayyana hakan ne ga manema labarai na fadar Villa bayan ya ganawar sa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a babban birnin tarayya Abuja.

A cewar gwamnan, sabbin kamfanin shinkafa takwas da aka kafa tun a shekarar da ta gabata sun taka rawar gani wajen bunkasa tare da wadatuwar shinkafa a kasar nan.

Gwamnan jihar kebbi; Atiku Bagudu
Gwamnan jihar kebbi; Atiku Bagudu

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, wannan abin yabo da Najeriya ta samu a halin yanzu yana da nasaba ne da jajircewar shugaba Buhari akan batun nan na sa na "lallai sai mun noma abinda zamu ci kuma mun ci abin da muka noma".

KARANTA KUMA: Hukumar INEC ta bakado wata cibiyar rajista ta boge a jihar Neja

Gwamnan ya ci gaba da cewa, ko shakka babu wannan shinkafa da Najeriya ke nomawa ta zarce ta kasashen ketare ta fuskar amfani ga kiwon lafiyar dan Adam, baya ga haka wannan hobbasa zai a gaza wajen habakar tattalin arziki na Najeriya.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, hukumar INEC ta bankado wata cibiyar rajista ta boge a yankin Arewacin Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: