Kotu ta daure mutane 63 da aka kama da hannu dumu dumu cikin rikicin jihar Kaduna

Kotu ta daure mutane 63 da aka kama da hannu dumu dumu cikin rikicin jihar Kaduna

Wata Kotun majistri dake titin Daura a cikin jihar Kaduna ta bada umarnin a daure mata mutane 63 da aka gurfanar a gabanta kan zargin hada hannu cikin rikicin kasuwar magani na jihar Kaduna.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito Alkalin Kotun Zainab Mohammed ta bada wannan umarni ne a ranar Alhamis 15 ga watan Maris, a shari’ar dake gabanta inda ake tuhumar mutane su 63 da hadin baki, tayar da zauni tsaye, daukan makami, raunata mutane da kuma kashe kashen rayuka

KU KARANTA: Dambawar siyasar APC ta ƙara zafafa: An fara nuna ma jutsa tsakanin Sanata Umoru da Gwamna Sani Bello

Alkalin Kotun ta bada wannan umarni ne zuwa lokacin da zata samu shawara game da yadda za’a cigaba da shari’ar daga daraktan shigar da kararraki na jihar Kaduna. Sa’annan ta dage sauraron karar zuwa ranar 5 ga watan Afrilu.

A farkon zaman Kotun, dansanda mai shigar da kara, Sufeta Sunday Baba ya bayyana ma Kotu cewar an kama mutanen ne da hannu cikin rikicin daya kaure tsakanin Musulmai da Kirista a kauyen Kasuwan magani

“Da misalin karfe 11 na safiyar ranar 26 ga watan Feburairu ne aka kira DPO na Yansandan yankin Kajuru, inda aka shaida masa ruruwar wata rikici tsakanin Musulmai da Kiristocin kauyen kasuwar magani, inda ya tura jam’an tsaro, wanda da isarsu suka tarar an kona gidaje da dukiyoyi da dama.” Inji shi.

Sufeta Sunday yace yansanda sun gano bama baman gargajiya guda hudu, baka guda biyu, kwari guda 11, gwafa guda 3, adduna biyu, bindigu guda uku da gora a inda suka kama mutanen. Sa’annan yace duk a wajen sun gano gawarwaki guda 12.

Sai dai Sunday yace bincike ya tabbatar musu da cewa shugaban gungun ya tsere, sa’annan ya bayyana laifin da ake tuhumar mutanen da cewa yayi karo da sashi na 59, 67, 190 da 78 na kundin hukunta manyan laifuka na jihar Kaduna.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng