Ina gwanin wani ga nawa: Ali Muhammad, dalibin da yafi samun nasara a jarabawar JAMB a Jigawa
Jaridar Rariya ta yi kicibus da wani hazikin dalibi dan asalin jihar Jigawa mai suna Aliyu Muhammad Sani Kaugama, wanda yafi kowa samun sakamako mai kyau a jarabawar JAMB da ya gudana.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Aliyu, dalibi a makarantar yara masu hazaka dake garin Bamaina ne ya samu maki 311 cikin maki 400 daya kunshi darussa guda hudu ya zamo dalibin da yafi maki a jihar Jigawa gaba daya.
KU KARANTA: Dakataccen dan majalisa Abdulmuminu ya koma bakin aiki a majalisa bayan kwanaki 108
Sai dai majiyar ta yi kira ga gwamnatin jihar Jigawa da ta jajirce wajen daukan nauyin wannan dalibi don cigaba da karatunsa a duk kasar data kamata, don al’ummar jihar Jigawa su amfane shi.

A ranar Talata 13 ga watan Maris ne dai hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandari na Najeriya, JAMB ta sanar da fitar da sakamakon jarabawar dake gudana a yanzu, inda ta fara sakin sakamakon daliban da suka zauna jarabawar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng