Ba makiyaya bane: Sojoji sun bankaɗo wasu yan bindiga a Filato, sun ƙwace makamai a hannunsu

Ba makiyaya bane: Sojoji sun bankaɗo wasu yan bindiga a Filato, sun ƙwace makamai a hannunsu

Rundunar Soja ta 3 dake jibge a jihar Filato ta samu nasarar cafke wasu yan bindiga guda bakwai tare da kwato makamai a hannunsu bayan wani rikici daya kaure tsakanin yan kauyen Miango da makiyaya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sojojin sun kama wadannan yan bindiga ne biyo bayan hare haren da suka kai ma yan Fulani makiyay a rugarsu dake kauyen Rafiki a ranar laraba 14 ga watan Maris, bayan sun samu kira daga mutanen kauyen.

KU KARANTA: Wani lauya da aka kama shi turmi da taɓarya yana zakke ma ƙaramar yarinya ya fuskanci hukuncin Kotu

Ba makiyaya bane: Sojoji sun bankaɗo wasu yan bindiga a Filato, sun ƙwace makamai a hannunsu
Yan bindigan

Sai dai a lokacin da Sojoji suka isa kauyen, sai yan bindigan suka bude musu wuta, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar Sojoji guda biyu, inda ba tare da wata wata ba Sojojin suka mayar da biki, suka kashe na kashewa, suka kama na kamawa guda 7.

Bayan da kura ta lafa, Sojojin sun gano gawarwaki har guda 23 a kauyen Mararaba Dare, tare da jama’a da dama da suka jikkata, hakazalika Sojoji guda biyu sun samu rauni wanda yasa aka garzaya dasu Asibitin runduna ta 3 don samun kulawa.

Ba makiyaya bane: Sojoji sun bankaɗo wasu yan bindiga a Filato, sun ƙwace makamai a hannunsu
Yan bindigan

Daga cikin makaman da Sojojin suka kwato akwai bindigar AK 47, karamar bindiga da alburusai da dama, a yanzu haka dai Sojoji sun bazama suna gudanar da sintiri a yankunan don kare sake aukuwar hare haren, kamar yadda Kaakakin rundunar Soja Bigediya Texas Chukwu ya sanar.

Ba makiyaya bane: Sojoji sun bankaɗo wasu yan bindiga a Filato, sun ƙwace makamai a hannunsu
Bindigarsu

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng