Christiano Ronaldo yayi Allah wadai da irin azabar da ake yiwa mutanen kasar Siriya

Christiano Ronaldo yayi Allah wadai da irin azabar da ake yiwa mutanen kasar Siriya

- Al'ummar kasar Siriya dai sun jima suna cikin tashin hankali da azabtarwa, idan rashin imanin bai kyale koda yara kanana ba

- Shahararren Dan wasan kwallon kafar nan na Real Madrid, Christiano Ronaldo ya yi Allah wadai da irin azabtar da al'ummar kasar ta Siriya da ake yi

- Dan wasan ya bada tallafin kayan abinci, tufafi da magunguna ga yara kanana da abin ya shafa

Christiano Ronaldo yayi Allah wadai da irin azabar da ake yiwa mutanen kasar Siriya
Christiano Ronaldo yayi Allah wadai da irin azabar da ake yiwa mutanen kasar Siriya

Shahararren dan wasan Real Madrid dinnan, Christiano Ronaldo, yana cigaba da iya bakin kokarin sa da bada tallafi domin sharewa al'ummar kasar Siriya hawayen su, kasar data share shekaru da yawa suna cikin tashin hankali.

DUBA WANNAN: Kididdiga ta kara tabbatar da cewa farashin masarufi na kara saukowa a Najeriya

Dan wasan, dan asalin kasar Portugal, Christiano Ronaldo ya jima yana tallafa wata kungiya mai kare hakkokin yara mai suna "Save the Children", yayi Allah wadai da irin yadda ake azabtar da yaran kasar Siriya, inda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ya ce: "Mutum ya zama mai karfin hali, sannan ya zama mai imani, kar mutum ya sake ya yanke kauna da samun rahamar ubangiji", inda daga bisa ni ya saka hotunan hare-haren da ake kaiwa al'ummar gabashin Guta na kasar Sham a watan Fabrairun wannan shekarar.

Dama dai shi Christiano Ronaldo din, ya jima yana bada tallafi ga al'ummar da suke cikin irin wannan rikici musamman ma yara kanana, inda yake basu tallafin kayayyakin masarufi, tufafi da magunguna.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng