Auren bogi: Hukumar shige da fice zata fara tantance ma su son yin aure
- Shugaban hukumar shige da fice ta kasa, Abdullahi Babandede, ya ce ana kulla auren bogi tsakanin bakin haure da 'yan Najeriya
- Shugaban hukumar ya ce maza bakin haure me su ka fi aikata wannan coge
- Babandede na wadannan kalamai ne yau a Abuja yayin wani taro da shugabannin shiyya na hukumar
Shugaban hukumar shige da fice ta kasa, Muhammad Babandede, ya ce ana kulla auren bogi tsakanin bakin haure da 'yan Najeriya a kasar nan.
Shugaban hukumar ya ce bakin haure maza su ka fi aikata wannan aure na bogi domin samun gindin zama a Najeriya.
Babandede na wadannan kalamai ne a yau Laraba yayin wani taro da shugabannin shiyya na hukumar a Abuja.
"Mun kula da wasu bakin haure, yawanci maza, dake aurar 'yan Najeriya domin samun izinin zama a Najeriya," inji Babandede.
Su na yin auren cogen ne domin domin gujewa duk wasu wahalhalun samun izinin zama a Najeriya saboda akwai sassauci ta fuskar biyan haraji ga duk wanda ke auren 'yar kasa.
DUBA WANNAN: Ba zan taba samun sukuni ba sai 'yan matan Chibok da na Dapchi sun samu 'yanci - Buhari
Babandede ya ce yanzu haka hukumar shige da fice ta kama wasu da aikata laifin auren bogin tare da bayyana cewar hukumar ta kara tsaurara matakan bayar da izinin zama a Najeriya.
Kazalika, ya ce hukumar daga yanzu hukumar zata sa ka idanu sosai da kuma tantance dukkan ma su son yin aure.
Babandede ya ce gwamnatin tarayya ta bakin ma'aikatar harkokin cikin gida ta bayyana irin wannan aure a matsayin barazana ga tsaron kasa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng