An tsaurara matakan tsaro a Damaturu gabanin zuwan shugaba Buhari

An tsaurara matakan tsaro a Damaturu gabanin zuwan shugaba Buhari

-Jami’an tsaro sun mamaye Damaturu gabannin zuwan Shugaban kasa Muhammadu Buhari

-Rotanni sun bayyan cewa an baza jami’an tsaro rike da makamai a wurare na yankin cikin gari, yayin da wasu kuma na sintiri cikin gari da motocin yaki da Hilux

-Manyan hanyoyi na garin musamman hanyar Maiduguri inda jirgin shugaban kasa zai sauka an rufesu

An tsaurara matakan tsaro a Damaturu gabanin zuwan shugaba Buhari
An tsaurara matakan tsaro a Damaturu gabanin zuwan shugaba Buhari

Jami’an tsaro sun mamaye garin Damaturu, babban birnin jihar Yobe gabannin zuwan shugaban kasa Muhammadu Buhari jihar ta Yobe, a safiyar yau.

Majiyar jaridar Daily Trust, ta bayyana cewa an baza jami’an tsaro rike da makamai a wurare na yankin cikin garin, yayin da wasu kuma nata sintiri cikin gari da motocin yaki masu garkuwa da Hilux.

KU KARANTA: An kama wata mata a Katsina bisa zargin kashe diyar kishiyarta

Manyan hanyoyi na garin musamman hanyar Maiduguri, inda ta nan ne jirgin shugaban kasa zai sauka an rufesu. Har Shaguna da wuraren kasuwanci dake kan hanyar an rufesu.

Malam Yusuf Balube, Dan siyasa ne, yayi korafin cewa hana mutane zuwa tarbar shugaban kasar zai bata masa suna a bangaren siyasa. "Kana gani hanyoyi duk an kaurace masu, mutane basu fito ba saboda yawan matakan tsaro," inji shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164