Yan bindiga sun kai hari Jos, sun kone gidaje da dukiyoyi
- Sabuwar rikici ya sake barkewa safiyar yau a garin Dong da ke Jihar Filato
- An kone gidaje biyu da motocci da dama, kana mutane da yawa na tattara kayan su suna barin garin
- Hukumar Yan sanda sun tabbatar da faruwar lamarin kuma sun aika jami'an su don kwantar da tarzomar
A safiyar yau Laraba ne mazauna garin Dong da ke karamar hukumar Jos ta kudu na jihar Filato suka bayar da rahoton wani hari da aka kai musu.
Wani mazaunin garin, Nanyah Raman, ya shaida wa Premium Times cewa sakamakon harin an kone gidaje biyu da motocci da dama.
"A halin yanzu da nake magana, ina iya jin karar harsashen bindiga, muna ta kiran lambobin hukumomin tsaro amma har yanzu bamu same su ba," inji shi
KU KARANTA: An kama wata mata a Katsina bisa zargin kashe diyar kishiyarta
Hukumar Yan sanda reshen jihar Filato ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta tura jami'an ta yankin domin kwantar da tarzomar.
Jami'in hulda da jama'a na yansanda, Terna Tyopey yace "Mun aike ta dukkan jami'an da muke dasu a yankin Rintiya zuwa garin na Dong, muna fatan abubuwa za su daidaita cikin kankanin lokaci, muna kira da al'umma su dena fargaba,".
Majiyar Legit.ng ta tattaro cewa mutane da dama sun tattara nasu-ya-nasu sun bar garin.
A yamancin Talata da ta wuce, Gwamna Simon Lalong ya yi magana ta bakin kwamishinan yada labarai, Yakubu Datti inda ya bayyana damuwarsa kan sabbin hare-haren da ake kaiwa kuma ya umurci jami'an tsaro su damko wanda ke da hannu cikin hare-haren.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng