Jamus ta baiwa rundunar sojin Najeriya kyautar jiragen yakin ruwa guda biyar
- Jamus ta yiwa rundunar sojin Najeriya kyautar jiragen yaki ruwa guda biyar
- Hafson rundunar sojin ruwa na Najeriya ya godewa kasar Jamus da kyautar da ta yiwa Najeriya
Kasar Jamus ta yiwa rundunar sojin Najeriya na ruwa kyautar jiragen yakin ruwa guda biyar, dan yakar ‘yan ta’adan da suka addabi yankin gabashin Arewa na tsakiya da kuma Tafkin Chad.
Jakdar kasar Jamus zuwa Najeriya, Ingo Herbert, ya mika jiragen a garin Onne dake jihar Ribas, yace kyautar zai kara karfin alaka tsakanin Najeriya da kasar Jamus.
Herbrt ya ce “Kyautar jiragen yakin ruwa guda biyar ga rundunar sojin Najeriya zai kara musu karfin gwiwar wajen yakar da ta’adaci a Najeriya.
KU KARANTA : Gwamnatin tarayya ta shirya kawo karshen jinya a asibitocin kasashen waje – Ministan kiwon lafiya
“Ba a yankin gabashin Arewa kadai jiragen za su yi amfani ba, hadda yankin Neja Delta za su yi amfani musamman wajen yakar masu satar mai, ,” Inji jakadan kasar Jamus.
Hafson rundunar sojin Najeriya, Vice Admiral Ibok Ete Ibas, ya godewa kasar Jamus da kyautar da suka yi musu da kuma taimaka musu wajen horas da sojojin ruwa 23 da suka yi a kasar Jamus.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng