‘Yan Matan Dapchi: Kungiyar BBOG za ta shiga Kotu da Shugaban kasa Buhari

‘Yan Matan Dapchi: Kungiyar BBOG za ta shiga Kotu da Shugaban kasa Buhari

- Kungiyar BBOG ta bada wa'adin ceto 'Yan matan Makarantar Garin Dapchi

- Lauyan Kungiyar yace za su nemi a hukunta Jamia'an tsaron da ke Yankin

- Falana yace akwai sakacin Hukuma wajen sace 'Yan Makarantar na Dapchi

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa za a maka Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari a Kotu lokaci ko kuma a garzaya Kotu da su a dalilin saken da aka yi na sace 'Yan makaranta a Garin Dapchi cikinJihar Yobe kwanaki.

‘Yan Matan Dapchi: Kungiyar BBOG za ta shiga Kotu da Shugaban kasa Buhari
Za maka Gwamnatin Shugaban kasa Buhari a Kotu

Kungiyar Bring Back our Girls wanda ta tsaya tsayin daka wajen ganin an ceto 'Yan matan Chibok da aka sace shekaru kadan da su ka wuce ne ke shirin shiga Kotu da Gwamnatin Tarayya bisa sakacin ta wajen satar yaran Makarantar Dapchi.

KU KARANTA: An nemi Shugaba Buhari ya kama tsohon Shugaba Obasanjo

Lauyan wannan Kungiyar ta BBOG watau Femi Falana ya bayyana cewa nan da mako guda za su zauna a Kotu inda za su nemi Gwamnati ta ceto 'yan Makarantar da aka sace sannan kuma a hukunta masu hannu wajen tsare yaran.

Kungiyar ta na gani akwai sakacin Hukuma wajen sace yaran makarantar saboda ganin cewa kusan hanya daya da aka bi wajen satar 'yan Makarantar da aka yi a baya aka kara amfani da shi wannan karo a Jihar Yobe bayan an zare Sojoji.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng