Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya cire shugaban hukumar afuwa, ya maye gurbinsa
Shugaba Buhari ya amince da cire shugaban hukumar shirin afuwa na yankin Naija-Dalta, Birgediya Janar Paul Boroh, tare da maye gurbinsa da Farfesa Charles Quaker Dokubo.
Farfesa Dokubo darekta ne a cibiyar bincike ta huldar kasa da kasa. Ya yi digiri na uku a kan hikimar tsara al'amura dake Bradford a Birtaniya, kuma dan asalin karamar hukumar Akuku-Turo ta jihar Ribas ne.
Kazalika, shugaban kasa, ya umarci mai ba shi shawara a kan harkokin tsaro ya gudanar da bincike kwakwaf a kan al'amura hukumar daga shekarar 2015 zuwa yanzu, musamman a kan zarge-zargen badakalar almubazzaranci da kudi da gwamnati ta ware domin shirin yafiya ga tsagerun yankin Naija-Dalta.
A wani labarin kuma kunji cewar gwamnatin tarayya ta sanar da cewar tana tattauna yadda zata ceto 'yan Najeriya daga kasar Libiya tare da tabbatar da cewar sun dawo gida lafiya.
Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, ne ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) hakan yau, Talata.
DUBA WANNAN: Da karfin tuwo wasu jami'an tsaro cikin farin kaya su ka yi awon gaba da ma'aikacin jaridar Daily Trust
Ministan ya ce ya gana da Jakadan kasar Libiya a Najeriya mai barin gado, Dakta Attai Alkhoder, wanda ya hayar da tabbacin samun hadin kan gwamnatin kasar.
Ya bayyana cewar gwamnatin tarayya na aiki tukuru domin tabbatar da kubutar 'yan Najeriya daga kasar Libiya tare da tabbatar da sun dawo gida lafiya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng