'Yan Matan Dapchi: Iyayen yara sunyi maraba da tsarin da shugaba Buhari ta sulhu da 'Yan ta'addar Boko Haram
-Iyayen ‘yan matan Dapchi da 'yan ta'addar Boko Haram su kai garkuwa dasu sunyi maraba da shawarar da shugaba Buhari ya kawo ta sulhu da 'yan ta'addar
-Iyayen yaran sunyi jawabi ga manema labarai a Damaturu, cewa shawarar ta kwantar masu da hankali na cewa yaran zasu dawo gida lafiya
A ranar Litinin dinnan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya tarbi ministan harkokin wajen Amruka, Rex Tillerson, shugaban ya fitar da sanarwar cewa gwamnatin tarayya ta yanke shawarar yin yarjejeniya da 'yan ta'addar Boko Haram domin ceto ‘ya matan da suka yi garkuwa dasu.
DUBA WANNAN: Majalisar Tarayya data Wakilai suna zargin junan su akan kasafin kudin 2018
Iyayen yaran sun ce sunyi murna bisa la’akari da shugaba Muhammadu Buhari yayi na yadda da yarjejeniyar sulhu ba tare da yin amfani da karfin Soji ba don ceto ‘yan matan.
Iyayen yaran sunyi jawabi ga manema labarai a Damaturu, cewa shawarar shugaban kasar ta kwantar musu da hankali, inda hakan ke nuni da cewa yaran zasu dawo gida lafiya.
Alhaji Bashir Manzo, shugaban kungiyar iyayen yaran, yace suna maraba da wannan tsarin sannan kuma suna farin ciki. Amfani da karfin soji zai iya janyo mutuwar da yawa daga cikin yaran, amma yarjejeniyar zata sanya su dawo mana gida lafiya.
Shugaban kasar ya bayyana hakan a jiya Litinin a lokacin da ya taryi ministan wajen Amurka Rex Tillerson, wanda ya kawo ziyara Najeriya a jiya, shugaban yace gwamnatin sa ta yanke shawarar yin yarjejeniya 'yan ta'addar Boko Haram din domin ceto 'yan matan wanda 'yan ta'addar suka yi garkuwa dasu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng