Zaman lafiya: Wasu makiyaya sun mika ma Yansanda bindigunsu guda 30 a jihar Neja

Zaman lafiya: Wasu makiyaya sun mika ma Yansanda bindigunsu guda 30 a jihar Neja

Wasu jama’an Fulani makiyaya sun mika nau’o’in bindiga guda 30 ga runsunar Yansandan jihar Neja kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Babban daraktan sashin kula da al’amuran manoma na jihar Neja, Alhaji Abdullahi Babayo ne ya sanar da haka cikin wata hira da yayi da kamfanin dillancin labaru a garin Minna a ranar Talata 13 ga watan Maris.

KU KARANTA: Duniya ina zaki damu ne? Yadda wata Mata ta hallaka wani dan jariri ta jefa gawar cikin masai

Babayo yace makiyayan sun mika makaman ne biyo bayan wani yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimmawa a tsakanin makiyaya da manoma, wanda sashin ya jagoranta, ya kara da cewa yanzu haka jami’ansa sun fara wayar da kan jama’a game da illolin satar shanu.

“Mun yi hadin gwiwa da malaman musulunci don sanin matsayin musulunci game da sata da kashe rai ba tare da hakki ba, kuma hakan ya taimaka matuka wajen rage masu aikata munana ayyuka, haka zalika muna kokarin janyo Fulani su fahimci addinin Musulunci da kyau, don cigabansu.” Inji shi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Babayo ya cigaba da cewa: “Muna iya bakin kokarinmu don ganin mun tsagaita fadace fadace tsakanin makiyaya da manoma, shiga iyakar gona, satar shanu da sauran munana laifuka.”

Daga karshe Babayo yayi kira da fitar da hanyoyin wucewar dabbobi, inda ya danganta rikicin da ake yawan samu da karancin hanyoyin, haka zalika yayi kira da gwamnati ta inganta ilimi, musamman na yayan manoma da na makiyaya, inda yace jahilci ma karfafa wannan fadace fadace.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng