Sai sojoji da dakarun CJTF sun yi lalata da mu kafin sun bamu isashen abinci – Masu gudun hijira sun rubutawa Buhari wasika
- 'Yan mata dake sansanin gudu hijira na Maiduguri sun zargi sojoji da yin lalata da su kafin su basu isashen abincin ci
- Rundunar sojin Najeriya sun karyata zargin da ake musu na cewa suna lalata da 'ya matan dake sansanin gudun hijiran Maiduguri
Wasu gungun mata dake sansanin gudun hijira a jihar Borno, sun rubutawa, shugaban kasa, Muhammadu Buhari budaddiyar wasika akan cin zarafin da sojoji da dakarun CJTF suke musu.
Matan da suka kai akalla 1320 sun zargi sojoji da CJTF da karban kudi a hannun su ko kuma su amince su yi lalata da su kafin su basu isashen abincin ci.
Matan sun ce sojoji basa barin su, su fita daga cikin sansanin su nemo abinci da za su ci, kuma ba sa wadata su da abinci har sai sun biya kudi ko su bari suyi lalata da su kafin su
KU KARANTA : Mun fara magana da mayakan kungiyar Boko Haram akan sako ‘yan matan Dapchi - Buhari
Rundunar sojin Najeriya sun karyata wannan zargi da aka yi musumusu, sun ce ana kokarin bata musu suna ne akan nasarar da suke samu akan mayakan kungiyar Boko Haram.
Matan sun roki gwamnatin tarayya ta sa a gaggauta sako mazaje da ‘ya’yan su da jami'an tsaro suka tsare su bisa zargi 'yan Boko Haram ne.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng